A jiya ne babbar kotun jihar Jigawa dake zamanta a karamar hukumar Birnin Kudu ta wanke wani mai suna Abubakar Garba da ake zargi da kashe abokinsa tare da sallamarsa.

An gurfanar da wanda ake zargin ne a shekarar 2018 bisa zargin yin amfani da gatari da kuma yi wa wani mai suna Abubakar Juli mummunan rauni wanda ya kai ga mutuwarsa.

Lamarin ya faru ne a kauyen Fulani na Maduba da ke karamar hukumar Buji inda aka kama shi aka gurfanar da shi a gaban kotu.

Da yake tabbatar da karar, lauyan mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu biyu yayin da wanda ake tuhuma ya bayar da shaida domin kare kansa.

Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Musa Ubale, ya ce hukucin laifin kisan kai shine kisa a karkashin sashe na 221 na kundin manyan laifuka na penal code na Jihar Jigawa.

Ya ce lauyan da ke kara ya gaza tabbatar da hujjojin nasa, don haka aka wanke wanda ake kara kuma aka sallame shi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: