Wata Babbar Kotun Jihar Jigawa wanda take zamanta a Birnin Kudu a jiya Juma’a ta yankewa Isa Ibrahim, hukuncin daurin rai-da-rai bisa samun sa da laifin yiwa wasu Yara Kanana Yan Gida Daya Fyade a kyauyen Kwari dake Karamar Hukumar Birnin Kudu.

Mai Gabatar da kara Shu’aibu Aminu, ya fadawa Kotu cewa a ranar 26 ga watan Satumba ne aka gabatar da Mutumin a gaban Kotu kan zargin yin lalata da Yaran Yan shekara 4 da 5 a Gonar sa.

Lauya mai gabatar da Kara ya gabatarwa da Kotu shaidu 5 wanda suke tabbatar da cewa mutumin ya aikata laifukan da ake zargin sa da su.

Da yake yanke hukuncin, Alkalin Kotun Mai Shari’a Musa Ubale, ya ce fyaden ya ci karo da sashe na 282 (1) na Manyan Laifuka wato Penal Code.

Kazalika, Mai Sharia Musa Ubale, ya yankewa Isah Ibrahim hukuncin bayan samun sa da laifukan da ake zargin sa da su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: