Wata kotun kasar Italiya ta yanke wa wani direban wani jirgin ruwa hukuncin zaman gidan yari na shekara guda saboda ya mayar da bakin haure zuwa kasar Libya bayan ya ceto su a tekun Bahar Rum.

An samu direban jirgin da laifin keta dokokin kasa da kasa, wanda ya hana mayar da kowa zuwa wajen da hakkinsa na dan adam ke fuskantar barazana.

Hukuncin ya ci karo da manufofin gwamnatin kasar Italiya da Tarayyar Turai.

Gwamnatin ta kasar Italiya da Tarayyar Turai na samar da tallafin kudaden aikin masu tsaron gabar tekun Libya yayin da suke tattara bakin haure tare da hana kwarararsu zuwa Turai.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun soki wannan tallafi na Tarayyar Turai, kuma sun sha yin rahoto kan irin mummunan yanayin da bakin haure ke fuskanta a kasar ta Libya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: