Wata Kungiyar a Arewacin Najeriya ta nemi Tinubu ya zaɓi Kiristan Arewa a matsayin mataimakinsa a zaben 2027
Wata ƙungiyar Musulmi daga Arewacin Najeriya mai suna Concerned Northern Muslim Ummah ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya zaɓi Kirista daga Arewa a matsayin mataimakinsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Bala Duguri, ya fitar, sun bayyana cewa sun gudanar da tattaunawa da ƙungiyoyin Musulunci daban-daban a Arewa, inda sakamakon ya nuna buƙatar daidaiton addini da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.
Duguri ya jaddada cewa, duk da nasarar da tikitin Musulmi-Musulmi ya samu a zaɓen 2023, lokaci ya yi da Musulmai masu ruwa da tsaki a siyasa za su nuna kyakkyawar niyya ta hanyar goyon bayan Kirista daga Arewa a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.
Ya kuma yi kira ga ‘yan takarar Musulmi masu neman wannan kujera a jam’iyyar APC da su janye domin bai wa Kirista dama, a matsayin sadaukarwa don haɗin kan ƙasa da kwanciyar hankali.
Sai dai wannan matsaya ta bambanta da ra’ayin wasu jiga-jigan jam’iyyar APC daga Arewa maso Gabas, musamman daga Jihar Borno, inda suka bukaci Shugaba Tinubu da ya ci gaba da aiki tare da Mataimakinsa na yanzu, Kashim Shettima, bisa la’akari da gudunmawar da ya bayar a gwamnatin. Wannan muhawara na nuna yadda batun daidaiton addini ke ci gaba da zama muhimmin abu a siyasar Najeriya, musamman ganin yadda tikitin Musulmi-Musulmi na 2023 ya jawo cece-kuce daga ƙungiyoyin Kirista da wasu ‘yan siyasa.