Wayyo: An samu Mummunan Haɗarin Mota a Hanyar Maigatari

0 460

A ƙalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a wani haɗarin mota da ya afku a hanyar Maigatari a ƙaramar hukumar Maigatari dake jihar Jigawa.

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Abdu Jinjiri, ya faɗa wa manema labarai a Jigawa ranar Litinin cewa wannan haɗari ya afku ne ranar Lahadi da kimanin ƙarfe 1:30 na rana, a cikin mota ƙirar Peugeot 206 da Golf 3.

Ya ce haɗarin ya afku ne bayan da tuƙi ya ƙwace wa direban Peugeot ɗin dake zuwa daga Kano, inda ya afka hannun da ba nasa ba, ya yi taho-mu-gama da wata Golf 3 dake tunkarowa.

Mista Jinjiri ya ƙara da cewa mutum bakwai dake cikin motocin sun mutu nan take, yayinda direbobi biyu da sauran fasinjoji takwas suka samu muggan raunuka.

“Jiya, da misalin ƙarfe 2 na rana, ‘yan sanda dake ƙaramar hukumar Maigatari, suka karɓi wani bayani cewa da misalin ƙarfe 1:30 na rana, wani mutum mai suna Rabilu Ahmad, ɗan shekara 30 mazaunin unguwar Ƙoƙi dake ƙaramar hukumar Dala ta Jihar Kano yana tuƙa Peugeot ƙirar 206 ruwan toka mai rijistar TRN 948, ya doshi Mala-Madori.

“Lokacin da ya je ƙauyen Kwalande dake ƙaramar hukumar Maigatari, sai tuƙi ya ƙwace masa ya tsallaka hannun da ba nasa ba, inda ya yi taho-mu-gama da wata motar dake tahowa ƙirar Golf 3 mai launin ganye da lambar FW 94 ABJ, wadda Mohammed Aminami, ɗan shekara 30 ɗan ƙaramar Hhukumar Dapchi ta jihar Yobe ke tuƙawa.

“A sakamakon haka, mutum bakwai dake cikin motocin suka mutu nan take, yayinda direbobin biyu da sauran fasinjoji tara suka samu raunuka”, in ji Mista Jinjiri.

A cewarsa, lokacin da suka samu bayanin haɗarin, sai ‘yan sanda suka garzaya inda haɗarin ya afku, suka kwashe gawarwakin da waɗanda suka ji raunuka zuwa Babban Asibitin Gumel dake ƙaramar hukumar Gumel.

Ya ce a halin yanzu waɗanda suka samu raunukan na kwance a asibiti suna kuma samun kulawa daga likitoci, yayinda ake ci gaba da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: