WHO ta ayyana sabon nau’in cutar Korona ta Omicron a matsayin wani abin damuwa ga duniya

0 125

Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO, ta ayyana sabon nau’in cutar korona a matsayin wani “abin damuwa” sannan ta rada masa suna Omicron.

Sabon nau’in cutar yana sauyawa da sauri, kuma bayanan da suka fara fitowa  game da shi sun nuna cewa akwai hatsarin karuwar sake kamuwa da shi.

Ranar 24 ga watan Nuwamba ne karon farko da aka bayyana wa WHO bullarsa daga afirka Ta Kudu, kuma an gano ya bulla a Botswana, Belgium, Hong Kong da isra’ila.

Kasashe da dama sun yanke shawarar takaitawa ko ma hana zuwa cikinsu daga Kudanci Afirka.

Birtaniya ta hana matafiya daga Afirka Ta Kudu, Namibia, Zimbabwe, Botswana, Lesotho da Eswatini shiga kasar sai dai idan ‘yan kasar ne ko kuma ‘yan yankin Island.

Jami’ai sun ce an hana jragen da suka fito daga Afirka Ta Kudu, Botswana, Zimbabwe, Namibia, Lesotho, Eswatini, Mozambique da Malawi daga shiga Birtaniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: