Ya kamata a dinga hukunta duk wanda ke amfani da kafafen sada zumunta wajen aikata laifi – Kashifu Inuwa

0 31

Gwamnatin Tarayya a zaman ta da kamfanin manhajar sada zumunta ta Tik Tok ta tabo batutuwa da dama da suka shafi tsaro, biyan haraji da tsaftar abubuwan da ake dorawa.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, wanda ya karbi tawagar kamfanin TIkTok jiya a Abuja, ya jaddada bukatar tabbatar da gaskiya, bin dokoki da ka’idoji a cikin amfani da kafofin sada zumunta don tabbatar da ingantaccen tsari mai kyau ba tare da keta doka ba, da yada labaran karya.

Isa Ali Pantami wanda Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) Kashifu Inuwa Abdullahi ya wakilta, ya ce kamata ya yi a hukunta duk wanda ke amfani da kafafen sada zumunta wajen aikata laifi.

Ya ce sharuddan da kamfanin Twitter ya amince da su kafin gwamnatin tarayya ta dage dakatarwar da ta yi masa, za a fadada su zuwa wasu kafafen sada zumunta da suka hada da TikTok.

Leave a Reply

%d bloggers like this: