Ya kamata gwamnati ta na bawa dalibai rancen kudi domin tallafa musu -Gbajabiamila

0 33

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi kira da a kafa bankin ilimi wanda zai ba da rancen kudi ga daliban da ke manyan makarantun gaba da sakandire ta yadda za a samar da tallafin ilimi a matakin da ya dace da kowa.

Ya kuma bayar da shawarar kafa tsarin lamuni na dalibai a kasar.

Kakakin ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a lokacin da yake gabatar da lacca karo na 52 na Jami’ar Legas, UNILAG.

Taron ya kasance mai taken: Gina yan baya da kyau da Samar da wani sabon samfuri na ilimin manyan makarantu a Najeriya a karni na 21.

Ya bayyana cewa a matsayinsa na dan majalisa kuma dan siyasa, daya daga cikin bukatu da ya saba karba a kodayaushe shi ne a ba shi kudin tallafin karatu na manyan makarantu, saboda makomar dalibai masu hazaka na iya shiga cikin hadari.

Ya yi kira da a hada kai tsakanin jami’o’i da masana’antu kamar yadda ake yi a kasashen da suka ci gaba da samar da ‘ya’ya masu kyau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: