Ya kamata ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar Jigawa su ɗauki ɓangaren majalisa a matsayin abokiyar tafiya wajen kawo cigaba – Jallo

0 152

Shugaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa, Barrister Abubakar Sadiq Jallo, ya shawarci ma’aikatu da hukumomin gwamnati jiha da su dauki bangaren majalisa a matsayin abokiyar tafiya wajen kawo cigaba a kowanne mataki.

Ya bada wannan shawara lokacin da ya ke tantance kiyasin kasafin kudin ma’aikatar shari’a na sabuwar shekarar 2020.

Barrister Abubakar Sadiq Jallo ya bayyyana bukatar wanzuwar kyakkyawar alakar aiki tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin tafiya kafada da kafada wajen gudanar da aikin gwamnati.

Ya lura cewa gabatar da rahoton zangon shekara ga majalisa dangane nasarori da kalubalen ma’aikatu da hukumomi zai bawa bangaren majalisar damar shiga tsakani akan lokaci domin tabbatar da ingancin aikin gwamnati.

Da yake tsokaci game da kiyasin kasafin kudin ma’aikatar shari’a, Barrister Abubakar Jallo, ya bada tabbacin aiki tare da kwamatin kasafin kudi na majalisar domin yin ‘yan gyare-gyare a kiyasin kasafin kudin ma’aikatar domin cimma bukatun bangaren shari’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: