‘Ya kamata yan majalisar kasa su gaggauta yanke hukunci akan kudirin dokar zabe’ -PDP

0 52

Gwamnonin da aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar PDP sun yi kira ga ‘yan majalisar kasa da su gaggauta yanke hukunci akan kudirin dokar zabe ta bara da ake takaddama akai.

Daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke cece-kuce akan kudirin, gwamnonin cikin sanarwar bayan taro da aka fitar bayan zamansu na jiya a Fatakwal ta jihar Rivers, sun ce ‘yan majalisar basu da wata mafuta face tsallake shugaban kasa ko kuma cire bangarorin da ake korafi akai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Disambar bara yaki amincewa da sanya hannu akan kudirin, inda yace kudaden da za a kashe wajen gudanar da zaben cikin gida kai tsaye shine dalilinsa na kin rattaba hannun.

Majalisar kasar za ta dawo zamanta a yau kuma kudirin dokar zaben shine kan gaba a batutuwan da za a tattauna.

Gwamnonin, a karkashin tutar jam’iyyar PDP, a hukuncin da suka yanke sun shawarci ‘yan majalisar da su duba yiwuwar tsallake Buhari domin gargadin shugaban kasar wajen aiwatar da makamancin hakan a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: