Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun sace mahaifiyar dan takarar sanata a Kano ta tsakiya karkashin jam’iyyar APC, Abdulsalam Abdulkarim A A Zaura.

Lamarin ya faru ne da safiyar Litinin inda ‘yan bindigar suka je gidan matar da ke Rangaza a kauyen Zaura a ƙaramar hukumar Ungogo suka sace ta.

Shugaban ƙaramar hukumar Injiniya bdullahi Garba Ramat, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaron da ke yanki ne suka sanar da shi.

Kazalika shugaban karamar hukumar ya rubuta a shafinsa na facebook cewa sun tashi da mummunan labarin sace mahaifiyar A A Zaura.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: