Yadda aka kama wani barawon mota dan shekara 22 a kauyen Yargaba dake Dutse

0 142

Wani barawon mota dan shekara 22, Surajo Husseni, a jiya ya sha da kyar daga hannun fusatattun matasa dake kokarin kashe shi a kauyen Yargaba dake yankin karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa.

Surajo Husseini ya saci wata mota mallakin Usman Aliyu Kandi wanda yake tsaka da aikin gyaran fitilar titi akan gadar sama ta garin Shuwarin dake yankin karamar hukumar Kiyawa ta jihar.

Yana tsaka da gyaran fitilar, matashin ya balle kofar motar, ya shiga ya tuka ta zuwa Kano, da nufin sayar da ita a wajen abokan harkarsa.

Jami’an hisbah bayan ceto matashin daga hannun fusatattun matasa, sun mika shi ga yansanda domin cigaba da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: