Yansanda a jihar Jigawa sun kama wata mata mai shekaru 25, mai suna Hadiza Musa, bisa zargin kashe mijinta.

Kakakin yansanda, Lawan Shisu Adam, ya tabbatar da kamen ga manema labarai a Dutse.

Yace lamarin ya auku a jiya da yamma a kauyen Maradawa dake yankin karamar hukumar Kazaure lokacin da wacce ake zargi tayi amfani da tabarya inda ta doke mijinta mai suna Isah Mohammed, sanadiyyar rashin jituwar da suka samu.

Shisu Adam yace mutumin ya samu munanan rauni a kansa lamarin da ya jawo mutuwarsa.

Yace an dauke shi zuwa babban asibitin Kazaure inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Ya tabbatar da cewa ana cigaba da bincike kuma za a gurfanar da ita a kotu nan bada jimawa ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: