Yadda aka rantsar da sojan da ya jagoranci juyin mulki a Burkina Faso a matsayin shugaban ƙasa na riƙon ƙwarya

0 184

An rantsar da sojan da ya jagoranci juyin mulki a Burkina Faso a matsayin shugaban ƙasa na riƙon ƙwarya. Sanye da kakin soja da jar hula, Paul-Henri Damiba ya ci alwashin yin aiki da kundin tsarin mulki yayin wani taƙaitaccen biki a babban birnin ƙasar, Ouagadougou.

Mista Damiba ya jagoranci dakarun soja wajen tumɓuke gwamnatin Shugaba Roch Kabore a watan da ya gabata suna masu zargin sa da gazawa wajen daƙile hare-haren masu iƙirarin jihadi.

Sojojin sun ce za su dawo da kundin tsarin mulki amma ba su faɗi lokacin dawo da mulkin farar hula ba. Yankin Afirka ta Yamma ya fuskanci jerin juyin mulki a ‘yan shekarun nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: