Wata kotun majistare da ke jihar Kano a jiya ta yanke wa wani matashi mai suna Aminu Rabi’u mai shekaru 18 hukuncin aikatau na kwanaki 14 bisa laifin satar wasu kaji biyu.

Aminu Rabi’u, wanda ke zaune a Unguwar Kwanar Bariki dake Kano, an same shi da laifuka biyu da suka shafi sata da kuma zaluntar dabbobi.

Mai gabatar da kara, Asma’u Ado, ta shaida wa kotun cewa wadda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Janairu a Unguwar Kwanar Bariki da ke Kano.

A wani labarin kuma, wani gini mai hawa daya da ake gyarawa ya ruguje a titin Audu Bako dake Kano.

Lamarin wanda ya faru jiya da safe, ana alakanta shi da amfani da kayan gini marasa inganci.

Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, an ce an samu asarar dukiya ta miliyoyin naira a lamarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: