- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Gwamnatin Jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ce tana bincike kan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta inda wasu ke raba man fetur a cikin jarakuna a matsayin kyautar halartar biki.
Kwamashinan Yaɗa Labarai na Legas, Gbenga Omotoso, ya ce “shakka babu wannan lamarin abin haɗari ne kuma zai iya jawo rasa rayuka da dukiyoyi”.
A ‘yan awannin da suka gabata ne bidiyon ya ɓulla, inda aka ga jarakunan fetur masu lita 10 a jere da za a raba wa mahalarta bikin. Daily Trust ta ce Chidinma Pearl Ogbulu ce ta shirya taron don murnar naɗa ta a matsayin Erelu Okin.
Yanzu haka ‘yan Najeriya na fama da ƙarancin man fetur, inda suke shafe awanni masu yawa a kan dogayen layuka.