Yadda barayi ko ‘yan bindiga suka kashe kwamishina; wani shugaban karamar hukuma ya ɓace a Kogi

0 167

A Najeriya, an harbe Kwamishinan Harkokin Fansho na jihar Kogi Mista Solomon Adebayo har lahira, yayin da Shugaban Karamar Hukumar Yagba ta Yamma, Pius Kolawole ya yi batan dabo.

Rahotanni sunce dukkan su biyun an kai musu hari ne a garin Erukutu dake kan iyakar jihar da Kwara da yammacin ranar Asabar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, ASP Williams Aya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce kwamishinan ya riga mu gidan gaskiya ne bayan harsashin maharn ya same shi.

Babu tabbas ko barayi ne ko ‘yan bindiga

To sai dai kakakin ya ce ba zai iya tabbatar da ko maharan ’yan fashi da makami ne ko masu garkuwa da mutane ko kuma ’yan bindiga ba.

Sai dai ya ce rundunar tasu ta lashi takobin ganin ta zakulo dukkan masu hannu a cikin lamarin.

ASP Williams ya ce tuni aka garzaya da gawar mamacin zuwa dakin adana gawarwaki, yayin da shi kuma kwamishinan har yanzu ake ci gaba da binciken inda ya shiga.

Shugaban Karamar Hukuma ya yi batan dabo.

“Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar Kogi, Mista Ede Ayuba ya umarci a aike da da dakaru domin kubutar da shugaban Karamar Hukumar daga hannun masu garkuwar da shi.

Rundunarmu zata hana idanunta bacci har sai ta kubutar da shi,” injin kakakin

An fara bindige masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya

ko a makon da ya gaba da sai da wani dan majalisar dattawan Najeriya ya tsallake rijya da baya bayan da ‘yan bindiga sukayi kokarin kashe har sau biyu ba tare da sunyi nasara ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: