Yadda Emefiele ya kwashe shekaru 3 ya nal karɓar dala miliyan 17.1 ta hannun wakilinsa – Shedar EFCC
Wani jami’in Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ya shaida wa wata kotu da ke Legas cewa Godwin Emefiele, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya karɓi kuɗi har dala miliyan 17.1 ta hannun wani wakili cikin shekaru uku.
Alvan Gurumnaan, wanda ya bada shaida a ranar Talata a gaban mai shari’a Rahman Oshodi na Kotun Musamman da ke Ikeja, ya ce an isar da kuɗaɗen ne tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023, kuma an ba da su ga Henry Omoile, abokin Emefiele, a gidan tsohon gwamnan CBN da ke Ikoyi.
Emefiele da Omoile na fuskantar tuhuma guda 19 da suka shafi karɓar cin hanci da bukatar rashawa da suka kai jimillar dala biliyan 4.5 da kuma naira biliyan 2.8.
Gurumnaan, wanda lauyan EFCC Rotimi Oyedepo ya jagoranta yayin bayar da shaidar, ya ce an gano inda kuɗin suka fito ne ta hanyar bayanan da wani direban daukar saƙo mai suna Monday Osazuwa ya bayar — wanda ya kasance shaida na farko a ɓangaren masu ƙara.
“Bisa ga cewarsa, Osazuwa ya bayyana cewa yana yin wasu ayyuka na sirri ga Emefiele, kuma a lokacin da ya kira shi, Emefiele ya aike masa da wani lambar waya ya ce ya kira wani mutum mai suna Mohit da ke London. Bayan ya kira Mohit, sai ya ba shi lambar wani mutum,” in ji shaida.
“Osazuwa ya hadu da wannan mutum daga watan Satumba 2020 zuwa 2023, inda ya karɓi kuɗaɗe a madadin Emefiele — jimillar su dala miliyan 17.1.
“Bayan ya karɓi kuɗin, Osazuwa kan je gidan Emefiele da ke Ikoyi ya mika kuɗin ga wanda ake tuhuma na biyu, Henry Omoile, kamar yadda wanda ake tuhuma na farko ya umurce shi.”
- Daily Nigerian Hausa