Yadda kasar Rasha ta karbe ikon birnin Kherson da ke kudancin kasar Ukraine

0 71

Rasha ta karbe iko da birnin Kherson da ke kudancin kasar Ukraine.

Da wannan tabbaci daga jami’an yankin, birnin Kherson na Ukraine ya zama babban birni na farko da ya fada hannun Rasha tun bayan mamayar kasar.

Kafofin yada labaran cikin gida sun bayar da rahoton cewa, yayin da ake cigaba da kai hare-haren bama-bamai, sojojin Rasha sun kai hari kan wasu makarantu uku da wani babban coci a birnin Kharkiv da ke arewa maso gabashin kasar, inda suka ce shaguna da dama da ke kusa da ginin majalisar birnin sun lalace.

Rahotannin sun ce a wani birnin mai suna Okhtyrka, gine-gine da dama sun ruguje sakamakon fashewar manyan bama-bamai.

Ba a samu rahoton wani yaji rauni ba.

A rana ta takwas da mamayar, kafofin yada labaran Ukraine sun ce an ji karar fashewar abubuwa da dama a Kyiv da safiyar yau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: