

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Kungiyar Hada kai da cigaban matasan masarautar Hadejia ta gudanar da taronta na shekara-shekara a sakateriyar Karamar Hukumar Kaugama.
A jawabinsa mataimakin gwamnan jiha Mallam Umar Namadi ya bayyana matasa a matsayin kashin bayan cigaban kowacce alumma
Mataimakin gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban karamar Hukumar Kaugama ya bukaci matasa da su marawa kudirorin gwamnati baya na hana aikata masha’a tare da kasancewa masu bin doka da oda
A sakon da ya aike da shi, mai martaba Sarkin Hadejia ta hannun Baraden Hadejia Ambassada Haruna Ginsau ya shawarci matasa da su guji dabi’ar wariyar yanki.
A jawabinsa na maraba shugaban kungiyar Comrade Muhammad Sani yace an kafa kungiyar ne domin hada kan matasa ayi tafiya da murya daya da nufin cigaban masarautar.
An gabatar da kasidu da kuma karrama wasu muhimman mutane a lokacin taron, ciki har da tsohon ministan harkokin waje, Dr. Nuruddeen Muhammad.