Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci wasu zababbun shugabannin jam’iyyar APC zuwa buda baki a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Wasu daga cikin shugabannin da suka hada da Musulmai da wadanda ba musulmai ba, da aka gayyata sun hada da tsohon gwamnan jihar Lagos kuma dan takarar shugaban aksa, Bola Tinubu, tare da tsaffin shugabannin jam’iyyar APC, Bisi Akande, John Ayegun da Adams Oshiomhole.

Daga cikin wadanda aka gayyata akwai tsaffin gwamnoni da Ali Modu Sheriff na jihar Borno, Bukar Abba Ibrahim na jihar Yobe, Sani Yermina na jihar Zamfara, Aliyu Wamakko na jihar Sokoto, Oserheimen Osunbor na jihar Edo, Olusegun Osoba na jihar Ogun da Murtala Nyako na jihar Adamawa.

Kazalika an gayyaci Abubakar Girei, Nasiru Dano, Fati Bala, Tijjanni Tumsah, Abba Aji, Lawal Shuaib da Mohammed Magoro.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: