Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun

0 105

Wani mutum a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, Ponle Adebanjo, ya kona matarsa, Lateefat, abin da ya kai ga mutuwarta saboda ta gudu ta bar shi a kan yawan dukanta da yake yi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Otun-Akute da ke jihar ta Ogun.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar , DSP Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce, a ranar Asabar da daddare ne mijin ya bi matar zuwa wani gida da ta koma a unguwarsu, ya tarar da ita tana sallah, ya kwara mata fetur ya cinna mata wuta.

A sanarwara da kakakin ‘yan sandan ya fitar ya ce, ganin haka ya sa ita ma matar ta kama mijin nata ta rike don su kone tare, har sai da mutane suka zo aka shiga tsakani.

Kakakin ya ce bayan an garzaya da matar asitbiti ne likita ya tabbatar ta rasu, shi ma kuma mijin daga baya ya rasu kamar yadda sanarwar ta tabbatar, bayan ‘yan sanda sun kama shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: