Wasu yan bindiga a jiya da daddare sun bindige wani dan kasuwa mai shekaru 47 da ake kira da suna Alhaji Tasi’u Abdulkarim a garin Tilden-Fulani dake yankin karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi.

Wani Kanin sa mai suna Isah Tilde ne ya tabbatarwa gidan telebijin na Channels faruwar lamarin inda yace, yan bindigar sun farwa wurin da marigayin yake sayar da magani a gari Tilden Fulani da misalin karfe 10 na dare, tare da karbar kudade masu nauyi a hannunsa, bayan sun kwace masa wayarsa ne suka tisa keyarsa zuwa wani wuri dake kusa da shagon sa tare da harbin sa har lahira.

A cewar wasu mazauna garin da abin yafaru sun bayyana cewa sinyji karar harbe harbe a lokacin da lamarin ya faru.

Jami’an yada labarai na rundunar yansadan jihar Bauchi Ahmed Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace sun harbe marigayin a lokacin da yake kokarin guduwa bayan anyi garkuwa da shi.

Ya kara da kwamsahinan yansandan jihar tini ya umarci DPO na kananan hukumomin jihar akan su tabbatar da cewa an damke wandanda suka aikata wannan lafin tare da gurfanar da su a gaban shariah.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: