Labarai

Yadda wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wasu maniyyata aikin hajji akan hanyarsu ta zuwa Sokoto daga karamar hukumar Isa ta jihar

Wasu ‘yan bindiga a jiya suka kai hari kan wasu maniyyata aikin hajji akan hanyarsu ta zuwa Sokoto daga karamar hukumar Isa ta jihar.

A yau ake sa ran maniyyatan zasu tashi zuwa kasa mai tsarki.

An rawaito cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kan ayarin motocinsu ne a dajin Gundumi amma jami’an tsaron da suka rako su sun dakile harin.

Wani mazaunin garin Isa, Malam Sirajo wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya ce maniyyatan sun tsallake rijiya da baya, kuma an dawo da wasu daga cikin su zuwa fadar Sarkin Gobir Isa.

Babban sakataren hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Sokoto, Shehu Muhammad Dange shi ma ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya ce bai da tabbacin ko an yi garkuwa da wasu.

Da aka tuntubi mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce bai san da harin ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: