Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani masallaci a garin Maisamari da ke karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba, inda suka kashe wani hakimi mai suna Alhaji Abdulkadir Maisamari.

Shaidu sun ce an kashe Alhaji Abdulkadir Maisamari ne a lokacin da yake Sallar Isha’i a daren jiya.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun bude wuta bayan sun kutsa kai cikin masallacin.

An ce mazauna garin sun tunkari ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa wani dutse da ke kusa da garin.

Wani mazaunin garin ya ce babu wanda aka sace, kuma an yi jana’izar hakimin kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Wannan masallacin shine na uku da aka kai wa hari a jihar Taraba ‘yan makonnin da suka gabata.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: