Yadda wata kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin sharar masallacin Juma’a na tsawon kwana 30 a jere saboda satar kur’anai guda 8

0 124

Wata kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a unguwar Fagge ‘Yan Alluna ta yanke wa wani mutum hukuncin sharar masallacin Juma’a na unguwar Fagge tsawon kwana 30 a jere saboda satar kur’anai guda 8 da ya yi.

Halifa Abdullahi wanda mazaunin unguwar Yola ne a birnin Kano, da ake zarga da fasa tagar masallacin Tudun Maliki a daren Lahadi tare da kwashe kur’ani mai tsarki guda takwas.

Masu gadin masallacin ne dai suka cafke wannan mutumi da ake zargi.

Masu gadin sun mika shi ga ofishin ‘yan sanda da ke filin Hockey, daga nan suka gurfanar da shi kotun shari’ar musuluncin.

Alkalin da ya yanke hukuncin, Bello Musa Khalid, ya yanke masa hukuncin sharar harabar masallacin da ke unguwar Fagge, wanda ke da girman gaske, har tsawon kwana 30 a jere.

Leave a Reply

%d bloggers like this: