Yan bindiga sun hallaka lauyan tsohon gwamna Jahar Anambara Nelson Achukwu.

Marigayin, an rawaito cewa an yi garkuwa da shi a gidan sa da ke Ukpor, a wata karamar hukuama da ke kudancin Jahar.

Al’amarin ya faru ne kasa da wata guda bayan lauyan yayi wani aiki a majalisar dokokin Jahar, inda daga bisani masu garkuwa da mutane sukayi awon gaba dashi.

Sawaba ta rawaito cewa an gano gawar lauyan sati biyu bayan anyi garkuwa da shi, inda masu garkuwa da mutanen suka wullar da shi tsakanin wasu kananan hukumomi biyu.

Wata majiya daga yan uwan mamacin ta ce an yi jana’izar sa aa jiya.

Kakakin runudunar yan sandar Jahar Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwan lamarin ya kuma ce ana yin bincike domin gano wadanda suka tafka wannan aika-aika.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: