Labarai

Yadda yan IPOB suka kashe ‘yan Arewa 10 ciki har da mace mai juna biyu da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a jihar Anambra

‘Yan haramtacciyar kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra, a ranar Lahadi sun kashe ‘yan Arewa 10, ciki har da mace mai juna biyu, da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a kauyen Isulo dake karamar hukumar Orumba ta Arewa a jihar Anambra.

An bayyana sunan matar da aka kashe da Harira Jibril mai shekaru 32, yayin da ‘ya’yan nata hudu suka hada da Fatima yar shekara 9 sai Khadija mai shekaru 7, da Hadiza ‘yar shekara 5 da Zituna mai shekaru 2.

Da yake bayyana yadda aka kashe matar tare da ‘ya’yanta, mijinta mai suna Jibril Ahmed, ya shaidawa BBC Hausa cewa ‘yan ta’adda sun far musu akan hanyarsu ta zuwa gida bayan sun ziyarci Orumba ta Arewa.

Shugaban Hausawa na garin Ihiala, Usman Abdullahi, shima ya tabbatar da harin, inda yace matar ‘yar asalin jihar Adamawa ce.

Yace dukanin Hausawa sun gudu daga Ihiala, biyo bayan yawaitar hare-haren da ake kai musu a yankin.

Gamayyar kungiyoyin Arewa cikin wata sanarwa tace hare-hare da kashe-kashe da lalata dukiyar ‘yan Arewa a sassa daban-daban na Kudu maso Gabas na faruwa ne sanadiyyar yada kiyayya da farfagandar da masu neman kasar ke yi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: