Yadda yan sanda ke farautar mutumin da yake yaudarar kauyuka wajen rusa masallatansu

0 62

An zargi wani mutum da yaudarar kauyuka da dama wajen rusa masallatansu, inda yake ce musu wata kungiyarsa mai zaman kanta ta kasar waje za ta gina musu manya a jihar Jigawa.

Daga zarar sun yarda da shi, sai ya gudu bayan ya kwashe kwanon rufi da tagogi da kofofin da ya cire daga masallatan.

Wanda ake zargin wanda ’yan sanda suka bayyana sunansa da Abba Haruna mai shekaru 21, ana zarginsa da sayar da kayayyakin.

Kakakin ma’aikatar shari’a ta jihar Jigawa, Abbas Rufa’i Wangara, ya shaidawa manema labarai cewa masallatai 14 ne abin ya shafa.

Wani basaraken gargajiya a daya daga cikin kauyukan, Usaini Wanzam Ilyasu, wanda shi ma ya zanta da manema labarai, ya ce wanda ake zargin sai da ya biya leburorin kudin aikin rusa masallacin kauyensu.

Ya ce mutumin ya bukaci masu yin bulo a kauyen da su fara kai bulon da za a yi ginin.

Amma bayan tafiyarsa, bai sake dawowa ba.

An kama shi ne bayan jami’an masallacin wani kauyen da ya je domin ya damfaresu suka kama shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: