Yan bindiga fiye da 200 sun kai hari garin Yangayya da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina

0 95

Wasu ‘yan bindiga kimanin 200, wadanda ake zargin sun fito ne daga sansanin shahararren dan fashin daji mai suna Dankarami, a jiya da tsakar dare, sun kai hari garin Yangayya da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Sun kashe dagacin kauyen, Jafaru Rabiu, tare da wasu mutane hudu.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da harin da kuma kashe-kashen.

Wani mazaunin garin Jibia, Halilu Kabir, ya shaidawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da tsakar dare inda suka yi ta aika-aika na tsawon sa’o’i uku.

Da manema labarai suka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isa, ya tabbatar da faruwar harin tare da kisan dagacin kauyen.

Ya ce an kashe mutanen kafin zuwan ‘yan sanda.

Gambo Isa ya kara da cewa ‘yan bindigar da ke addabar yankunan Jibia zuwa Batsari zuwa Safana zuwa Danmusa a jihar sun fito ne daga jihar Sokoto.

Leave a Reply

%d bloggers like this: