‘Yan Bindiga Sun Kashe Akalla Mutane 9 A Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna

0 85

Akalla mutane tara ne aka ruwaito ’yan bindiga sun kashe a wani hari a kauyen Ungwan Dakwa da ke kusa da unguwar Dogon Dawa a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Duk da cewa rundunar ’yan sandan jihar ba ta ce uffan kan lamarin ba, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Gwari, Yahaya Birnin Gwari, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ’yan bindigar sun dirar wa al’ummarsa ne da misalin karfe 2 na ranar Asabar, inda nan take suka bude wuta kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ce wasu mutanen kauyen sun samu raunuka a harin, amma an garzaya da su asibitocin da ke makwabtaka da Funtuwa a Jihar Katsina domin yi musu magani, yayin da akasarin mutanen kauyen suka tsere saboda fargabar kawo sabon hari .

Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin Arewa Maso Yamma da ke fama da matsalar ’yan bindiga.

Hare-hare da sace-sacen jama’a domin karbar kudin fansa na ci gaba da kamari tun bayan kammala zabe a watan Fabrairu da Maris. Wasu ’yan bindiga sun kashe mutane 33 a wani hari da suka kai wani kauye da ke Kaduna a watan da ya gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: