Hukumar kula da shige da fice ta kasa reshen jihar Jigawa ta bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe jami’inta 1 tare da raunata wasu 2 a karamar hukumar Birniwa.

Kwanturolan hukumar na jiha Ismail Abba ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai akan faruwar lamarin jiya a Dutse, babban birnin jiha.

Ismail Abba ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin karfe 11 da mintuna 20 na rana, lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari kan daya daga cikin sansanonin hukumar da ke yankin Birniwa zuwa Galadi.

Kwanturolan ya kara da cewa an kai jami’an da suka jikkata zuwa asibiti domin duba lafiyarsu, yayin da aka binne jami’in da ya rasu.

A cewarsa, za a mika babura da wayar hannu da aka jefar ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike tare da daukar mataki.

Ismail Abba, ya ce uku daga cikin ‘yan bindigar su 6 sun tsere daga harin ba tare da wani rauni ba.

Ya yi zargin cewa ‘yan bindigar sun fito ne daga makwabciyar kasar Jamhuriyar Nijar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: