Yan Bindiga sun kashe mutane 3 a wani hari da suka kai kan hanyar Kaduna zuwa Zaria ta Karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Yan bindigar da farko sun kewaye kyauyen Dunki wand yake kan hanyar Kaduna, tare da fara harbi babu kakkautawa, inda nan take suka kashe mutane 2 mazauna garin.

Kwamishina Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida naq jihar,Samuel Aruwan, shine ya bayyana hakan, inda yace Dakarun Sojojin da suke aiki a babbar hanyar sun hangi yan Bindigar a lokacin da suke kokarin kaiwa hari zuwa Kyauyen Sharu.

A cewarsa, bayan samun bayanan sirri, Sojoji sun fafata da yan bindigar, inda suka raunata wasu daga cikinsu a kyauyikan Lambar Zango da Hawan Kwaranza.

Kwamishinan ya ce duk da irin kokarin da Sojojin sukayi yan bindigar sun kashe wani Matafiyi, wanda ba’a bayyana sunansa ba, tare dayin awun gaba da Shanun mutanen garuruwan Mashashiya da Farguza wanda suka sace.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: