‘Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da dama a jihar Zamfara

0 304

‘Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da dama a wani hari da suka kai kan wasu matafiya a jihar Zamfara.

Harin ya faru ne a yankin Jibia da ya hada jihohin Katsina da Zamfara.

An ce ‘yan bindigar sun bude wuta kan motocin da ke tafiya, wanda hakan ya tilasta musu tsayawa.

Matafiya suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako ta Zurmi daga Gurbin Bore.

Wani mazaunin garin, Jamilu Gambo, wanda aka kashe surukinsa yayin harin, ya ce ‘yan fashin sun fi 50.

Jamilu Gambo, wanda ya ce suna binne mamatan lokacin da wani dan jarida ya kira shi da misalin karfe 11 na safe, ya ce maharan ne suka sace dukkan sauran matafiyan.

Ya kara da cewa ‘yan fashin ba su tuntubi wani ba don neman kudin fansa ga wadanda suka sace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: