‘Yan bindiga sun kashe wasu manoma 4 tare da yin garkuwa da wasu mutum 8

0 215

Wasu  da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wasu manoma  hudu tare da yin garkuwa da wasu mutum takwas daga kauyen Nahuta da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina a ranar Asabar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da kai harin a jiya Lahadi a Katsina.

Yace manoman suna girbin amfanin gonakinsu ne a lokacin da maharan suka far musu. Ya kuma kara da cewa daya daga cikin manoman da yayi nasarar tserewa yayin kai harin ya samu raunuka sakamakon harbin ‘yan bindigar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: