’Yan bindiga sun nada mambobinsu a matsayin dagatan wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato

0 89

’Yan bindiga sun nada mambobinsu a matsayin dagatan wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato.

A cewar wata jaridar internet da ke Sokoto, rahotanni sun ce sabbin shugabannin kauyukan na ‘yan ta’addan na yin aiki ne bisa umarnin daya daga jiga-jigan yan fashin mai suna Turji.

A cewar rahoton, ‘yan fashin dajin sun fara kiran mutanen kauyen Gangara zuwa wani muhimmin taro a kauyen Saturu domin sanar da sauke shugabannin kauyukan tare da nada wasu daga cikin mambobinsu a matsayin sabbin hakimai.

Wadanda suka halarci taron kwamandojin Turji ne su biyar, wadanda suka hada da Dan Baƙarlo da Boka Tamiskwe da Hassan Ɗan Ƙwaro da Dogo da Jammu Baƙi.

Daga nan sai ’yan bindigar suka bukaci mazauna kauyen Gangara da su zabi daya daga cikin kwamandojin ‘yan fashin dajin guda biyar da zai yi aiki a matsayin dagacin kauyen.

Mutanen kauyen sun zabi Ɗan Baƙƙwarlo, bayan da sabon dagacin ya ba su wasu sharudda da umarnin sake bude wasu kasuwanni da masallatan Juma’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: