‘Yan Bindiga Sun Sace Kwamishiniyar Hukumar Kula Da Yawan Jama’a Ta Kasa A Jihar Ribas

0 75

‘Yan bindiga sun sace wata kwamishiniyar hukumar kula da yawan jama’a ta kasa, Gloria Izonfuo, a jihar Rivers.

Mai magana da yawun yansanda a jihar ta Rivers, Grace Iringe-Koko, wacce ta tabbatar da lamarin a jiya, tace an sace Gloria Izonfuo a ranar Lahadi tare da direbanta da wata ‘yar aiki a mahadar Ogbakiri a kan titin Gabas zuwa Yamma.

Mutane ukun na kan hanyar dawowa Fatakwal, babban birnin jihar Rivers, bayan wata tafiya da suka yi zuwa garin Brass a jihar Bayelsa, lokacin da aka sace su.

Grace Iringe-Koko ta kara da cewa an aika da tawagar ‘yansanda domin tabbatar da cewa sun ceto kwamishiniyar da yaranta.

Gloria Izonfuo tsohuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin jihar Bayelsa ce.

Tuni wadanda suka sace ta suka nemi diyyar naira miliyan 500 domin sakinta da yaranta. Gloria Izonfuo na tsaka da shirye-shiryen aikin kidaya a jihar Bayelsa cikin makonnin biyun da suka gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: