‘Yan bindiga sun sake sace mahaifiyar dan majalisar dokokin jihar Kano

0 8

‘Yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun sace mahaifiyar shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano, Isyaku Ali, a garin Gezawa.

Dattijuwar mai suna Hajiya Zainab, tana zama gida daya tare da wasu ‘yan’uwa da masu aikatau. Dan ta, Isyaku Ali, ya taba zama kakakin majalisar dokokin jihar.

Wani dan dan majalisar, Saminu Ali, ya shaidawa BBC Hausa cewa ‘yan bindigar sun mamaye gidan da misalin karfe daya na dare a jiya.

Yace ‘yan bindigar, dauke da muggan makamai, sun tursasawa wasu ‘yan’uwa akan su kai su bangaren gyatumar a gidan.

Manema labarai sun rawaito dan majalisar na cewa ‘yan bindigar sun balla kofar bangarenta bayan taki amincewa ta bude musu.

Yace daya daga cikin masu yi mata aiki ne yayi shelar lamarin, daga baya kuma aka sanar da ‘yansanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: