Yan bindiga sun sake sace mutane 10 a garin Jere wanda ya ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna

0 39

Yan bindiga sun sace mutane 10 a garin Jere wanda ya ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a jiya Lahadi da Daddare.

Manema Labarai sun rawaito cewa yan bindigar sun shiga garin ne ta Unguwar Ma’aji, inda suka dinga karya gidaje tare da yin garkuwa da Mutane da kuma Yara Kanana.

Wani mutum wanda aka sace Makocinsa ya bayyana cewa yan bindigar sun je garin ne da misalign karfe 10 na Dare inda suka sace mutane 14.

A cewarsa, mutane 3 daga cikin wadanda aka sa ce sun tsere, tare da barin wata Mace 1 a cikin Daji a lokacin da yan bindigar suka fuskanci bata da Lafiya.

Haka kuma ya ce yan bindigar sun sace Alhaji Kasuwa da Matarsa Aunty Kubacha da kuma dan su, kazalika sun sa ce wani mai suna Malam Sule Maishago da kuma Iyalan gidansa.

Majiyar ta ce a lokacin da yan bindigar suka shiga garin sun kira Jami’an tsaro domin kawo musu dauki, sai dai basu zo ba har zuwa lokacin da yan bindigar suka ci karen su, ba babbaka suka tafi.

An tuntubi Kakakin rundunar yan sandan Jihar Kaduna Muhammad Jalige, sai dai bai daga wayar da aka masa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: