Mahaifiyar wani dan majalisar dokokin jihar Kano, Isyaku Ali, da aka sace, ta shaki iskar ‘yanci bayan biyan kudin fansa na naira miliyan 40.

‘Yan bindiga sun sace Hajiya Zainab a ranar 12 ga watan Janairu a gidanta dake karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Dan ta, Isyaku Ali, tsohon kakakin majalisar dokokin ne kuma a yanzu shine shugaban masu rinjaye a majalisar.

A yau da safe, dan majalisar ya tabbatar ta sakin mahaifiyar ta sa ga manema labarai a Kano. Yace shi da wasu mutane suna kan hanyarsu ta zuwa dauko ta a jihar Jigawa inda barayin suka sake ta.

A wani labarin kuma, jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano, karkashin shugabanci Abdullahi Umar Ganduje, da kada ta yi amfani da kisan Hanifah a matsayin hanyar tatsar kudade daga masu makarantun kudi.

Biyo bayan kisan Hanifah Abubakar yar shekara 5 a hannun Abdulmalik Abubakar, mamallakin makarantar Noble Kids dake yankin karamar hukumar Nasarawa ta jihar, gwamnatin jihar ta soke dukkan lasisin makarantun kudi a jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: