Yan bindiga sunyi garkuwa da wata mata mai shayarwa a jihar Bauchi

0 104

Bayan rahotan da muka kawo muku makonni 2 da suka gabata a kauyen Birshin Fulani dake kusa da birnin Bauchi inda wasu yan bindiga suka kashe mutane 2, yanzu haka wasu yan bindigar sunyi Garkuwa da wata mata mai shayarwa mai suna Rukayya Odedoyina.

A cewar kamfanin dillacin labarai na kasa NAN yan bindigar da suka kai su 10 sun farwa matar ne a gidanta da misalin karfe 12 na ranan yau inda sukayi awun gaba da ita, kuma suka yasar da yayanta kanana su 3 a farfajiyar gidan.

Hakan ne yasa wasu mazauna kauyen suka shiga zanga zanga saboda halin rashin tsaron da suke fuskanta.

Masu zanga zangar dake dauke da ganye a hannayensu anjiyo su suna cewa “Bamu yarda ba” tare da kira  ga gwamnati akan tashiga lamarin.

Kawo yanzu rundunar yansadan jihar Bauchi batace komai ba akan wannan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: