‘Yan bindigan da suka yi garkuwa da wani Kansila hade da mutum 9 a jihar Sokoto sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 60

0 106

‘yan bindigan da suka yi garkuwa da mutane 9 da suka hada da Kansila mai wakiltar mazabar ‘Yar Tsakuwa a karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto, sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 60.

Wani mazaunin kauyen ‘Yar Tsakuwa, Nazifi Abdullahi, ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kira iyalan wadanda abin ya shafa suka bukaci su tara kudin.

An bayyana cewa ‘yan bindigan sun kai farmaki ‘Yar Tsakuwa ne da misalin karfe 12 na safiyar ranar Asabar, inda suka rika gudanar da aika-aika har zuwa karfe 3 na dare.

Kuma suka yashe gidaje da shaguna tare da sace babura da kayayyakin abinci da magunguna da sauransu.

Bata-garin wadanda tun farko suka yi awon gaba da mutane 20, sun sako 11 daga cikinsu kafin su tsere zuwa sansaninsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: