Yan bindigan da suka yi garkuwa ‘yan biki 29 a jihar Sokoto sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 145 kafin a sake su

0 75

‘Yan bindigan da suka yi garkuwa ‘yan biki 29 a ranar Asabar a jihar Sokoto, sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 145 kafin a sako su.

Wannan ya fito ne ta bakin babban sakataren kungiyar masu sayar da waya a jihar, Nasiru Musa.

Yawancin wadanda aka yi garkuwa da su dillalan wayar salula ne a kasuwar waya ta Bebeji da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

An yi garkuwa da su ne da yammacin ranar Asabar a lokacin da suke dawowa daga daurin auren daya daga cikin abokan aikinsu a Tambuwal a jihar Sokoto.

Jim kadan bayan sace su, an yi tunanin an sace mutane 50 amma da dama daga cikin wadanda ake tunanin an sace sun koma gida. Wasu 7 kuma’yan banga da ke aiki a yankin ne suka kubutar da su.

Shugaban kungiyar Mustapha Khalifa ya shaidawa manema labarai cewa wasu daga cikin su da suka kubuta a lokacin da ake garkuwa da su suna karbar magani a babban asibitin Talatan Mafara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: