Yan bindigar da suka kai hari tare da sace fasinjoji a jirgin ƙasa Kaduna zuwa Abuja sun sako karin wasu 11 daga cikinsu

0 91

Yan bindigar da suka kai hari tare da sace fasinjoji a jirgin ƙasa Kaduna zuwa Abuja sun sako karin wasu 11 daga cikinsu

Mutum 11 ‘yan fashin suka sako saɓanin alƙawarin da suka yi tun farko cewa, za su sako dukkan matan da suke tsare da su, kamar yadda mawallafin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu ya ruwaito.

Tukur wanda shi ne mai shiga tsakanin Yan bindigar da kuma gwamnatin tarayya, ya ce mata shida ne da kuma maza biyar aka sako a yanzu bayan shafe tsawon loƙaci ana tattaunawa.

Wadanda aka sako din sunhada Amina Ba’aba Mohammed, Rashida Yusuf Busari, Jessey John, Hannah Ajewole
Amina Jibril, Najib Mohammed Dahiru, Hassan Aliyu, Peace A. Boy, Danjuma Sa’idu, Gaius Gambo da kuma wani Yaro karami da ba’a bayyana sunansa ba.

Idan za’a iya tunawa a ranar 6 ga watan Afrilu Yan bindigar suka saki manajan Bankin Noma na kasa Alwan Hassan bayan an biya Naira Miliyan 100 a matsayin kudin fansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: