Yan bindigar sun kashe mutane 3 a wani hari da suka kai garin Gada na karamar hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara.

A lokacin da suka kai harin na yau yan bindigar sun kashe Hakimin Gada Alhaji Umaru Bawan-Allah da kuma yayan sa biyu.

Wani mazaunin garin wanda lamarin ya faru a gaban idanun sa, ya fadawa gidan Talabijin na Channels Tv cewa, yan bindigar sun kewaye garin ne daren wayewar garin yau Laraba.

A cewarsa, yan bindigar sun sace mutane da dama, baya ga kashe Hakimin Garin na Gada da kuma yayan sa biyu.

Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai na Jihar Zamfara Malam Ibrahim Dosara, ya tabbatar da kaiwa harin ga Gidan Talabijin na Channels Tv.

Ibrahim Dosara ya ce bayan kashe Hakimin da Yayansa, yan bindigar kuma sun kone gidan Hakimin.

Kwamishinan, ya ce hukumomin tsaro ciki harda Sojojin Sama sun fatattaki yan bindigar daga garin su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: