‘Yan Boko Haram sun kai hari wani sansanin soji a Borno

0 89

‘Yan bindigar da ake zargin mayakan tsagin kungiyar Boko Haram ne na ISWAP sun kai hari kan wani sansanin soji a kudancin jihar Borno.

Kungiyar ta mamaye garin Damboa da misalin karfe 10 da rabi na safe, cikin gomman motocin yaki.

Lamarin ya jefa garin cikin rudani kasancewar mazauna garin da yan gudun hijira na gudun neman tsira.

Kamar yadda wata majiya ta bayyana, an aiko da jiragen sama na yaki domin taimakawa dakarun sojin dake kasa tare da yan kato da gora.

Damboa na da nisan kilomita 100 daga Maiduguri, cibiyar rikicin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: