‘Yan gudun hijira miliyan ɗaya sun samu takardun izinin zama daga ƙasashe 38 daga shekarar 2019 zuwa 2023

0 164

Fiye da ‘yan gudun hijira miliyan ɗaya daga ƙasashe takwas masu yawan samun neman mafaka sun samu takardun izinin zama daga ƙasashe 38 daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Rahoton hadin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyar Haɓɓaka Tattalin Arziki da Haɗin Kai ta Duniya ya nuna cewa, izinin shiga ƙasashen ya gudana ta hanyoyin neman aiki, da neman karatu, da neman haɗuwa da dangi.

A shekarar 2023 kadai, an ba da izini fiye da 255,000, mafi girma tun da aka fara bin diddigin lamarin a shekarar 2010. Kasashe irin su Jamus, da Kanada, da Amurka, da Birtaniya da Sweden na cikin manyan ƙasashen da suka bayar da irin wannan dama, yayin da MDD ke kira da a sauƙaƙa hanyoyin samun izini ga ‘yan gudun hijirar da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa domin magance matsalolin da ke haifar da gudun hijirar.

Leave a Reply