’Yan kasuwar Raguna na nuna damuwa kan ƙarancin saye da sayarwa gabanin bikin Babbar Sallah
’Yan kasuwar rago a kasuwar dabbobi ta Shuwarin da ke ƙaramar hukumar Kiyawa a nan Jihar Jigawa sun koka da ƙarancin saye da sayarwa kafin bikin Babbar Sallah, duk da tsadar farashi da ƙarancin dabbobi.
Rahoton jaridar The Guardian da ya tattara a ranar Litinin, ranar kasuwa, ya nuna cewa ’yan kasuwa suna danganta wannan matsala da ci gaba da rufe iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya kawo cikas ga shigo da dabbobi daga waje.
Farashin raguna a kasuwar ya kai daga Naira dubu 180,000 zuwa Naira dubu 980,000, inda mafi ƙasƙancin farashi ke kai Naira dubu 160,000.
Wasu dabbobin kamar raƙuma da tumaki na farawa daga Naira dubu 780,000 zuwa sama da miliyan ɗaya ga kowanne raƙumi.
Wannan na faruwa ne duk da ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen sauƙaƙa harkar cinikayya da makwabciyarta ta arewa. Mal. Sale Shuwarin, wani ɗan kasuwa a kasuwar Shuwarin, ya bayyana wasu dalilai da ke haddasa hauhawar farashi.
A cewarsa, Raguwar darajar Naira na daga cikin manyan dalilan hauhawar farashin raguna.
Rahotanni daga kasuwa sun nuna cewa an sami dan saukin farashi a makonnin baya. Duk da wannan dan sauki, ’yan kasuwa na nuna damuwa da ƙarancin masu zuwa sayayya da kuma tasirin da hakan zai iya haifarwa a lokacin bukukuwa.