Yan kungiyar IPOB da ke kudancin Najeriya ne suka kulla mini sharri – Abba Kyari

0 106

Fitaccen dan sandan nan da aka tsare a baya-bayan nan kan badakalar hodar Iblis, DCP Abba Kyari, ya zargi kungiyar IPOB da ke Kudancin kasar nan da kulla masa sharri da makarkashiya.

Abba Kyari ya ce IPOB da reshenta na ESN ne suka kulla masa sharri da nufin bata masa suna, saboda ragargazar su da ya rika yi a yankin Kudu masa Gabashin Najeriya.

Ya yi zargin ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin da Hedikwatar ’Yan Sandan kasa ta kafa domin binciken zargin da ake masa na saba ka’idar aiki.

Kwamitin wanda Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Joseph Egbunike, yake jagoranta, ya yi watsi da zargin na Abba Kyari a matsayin soki-burutsu.

Rahoton kwamitin ya kara da cewa Abba Kyari bai musanta cewa ya yi kunnen kashi ba wajen saba dokar aikin dan sanda a yadda ya rika amfani da kafofin sada zumunta, duk kuwa da cewa an sha yi masa gargadi a kan hakan.

Rahoton kwamitin dai shi ne wanda babban Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya mika wa Hukumar Aikin Dan Sanda, da ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi daga DCP zuwa ACP.

Duk kokarin jin ko Hukumar Aikin Dan Sanda ta yi watsi da rahoton da aka mika mata sun shekarar da ta gabata, kamar yadda ake rade-radi, amma abin ya faskara. Har kawo lokacin hada rahotan Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani, bai amsa kiran waya ba,

Idan ba a manta ba, Abba Kyari na kuma fusknatar zargin alaka da Badakalar Hushpuppi, wadda ta danganci damfara ta daruruwan miliyoyin daloli a kasashen waje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: