

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau shugaban kwamitin Masallacin Rukunin Gidajen Yan Majalisar Najeriya na Apo, ya ce sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin gaba ɗaya.
Sanata Dansadau ya shaida wa BBC Hausa cewa sabon matakin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid din ne a ranar Asabar 2 ga watan Afrilun nan.
A wata wasiƙa da kwamitin masallacin ya fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Sanata Dansadau da aka aike wa Digital Imam, ya ce an ɗauki matakin korarsa ne gaba ɗaya saboda ƙin yin nadamar da Sheikh Nuru ya nuna bayan dakatar da shi ɗin.
Wasiƙar ta ce: “Akaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara ɗabi’ar mutum.
“Abin takaici, martanin da ka mayar kan dakatarwarka ta nuna cewa, balle ma har ka nuna nadama kan abubuwan da ka faɗa.
“Shugabanci na buƙatar sauke haƙƙi ka’in da na’in. Idan kalamanmu sun ɓata wa ƴan ƙasa rai fiye da faranta musu, to akwai hakki a kanmu na ɗaukar matakin da ya dace saboda al’umma.
“Ga dukkan alamu kuma kamar ba ka da niyyar gyara huɗubarka ta ranar Juma’a ta yadda za ta yi daidai da halin rashin tsaro da ake ciki a Najeriya,” in ji sanarwar.
BBCHausa